Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta harbo jirgin sama maras matuki ciki kirar “Hermes 450” na ‘yan sahayoniyya a sararin samaniyar garin Taybeh
A ci gaba da goyon bayan al’ummar Falastinu masu gwagwarmayar neman ‘yanci a Zirin Gaza da jaddada goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da kuma kare kasar Lebanon da al’ummarta daga wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, mayakan kungiyar Hizbullah sun kai kakkabo jirgin saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar “Hermes 450” a sararin samaniyar garin Taybeh.
A sanarwar da kungiyar gwagwarmayar Musuluncin ta kasar Lebanon ta fitar ta tabbatar da cewa: Mayakanta sun kai harin ne da makami mai linzami, kuma sun yi nasarar harbo jirgin, inda aka gan shi yana cin wuta.
Har ila yau, ‘yan gwagwarmayar ta Hizbullahi sun sanar da cewa: Sun kai hari kan matsugunin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gid ana “Kiryat Shmona” da makamai masu linzami.