MDD :  kashi 70 cikin 100 na wadanda aka kashe a Gaza yara ne da mata

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR) ya ce kashi 70 cikin 100 na wadanda aka kashe a zirin Gaza a yakin

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR) ya ce kashi 70 cikin 100 na wadanda aka kashe a zirin Gaza a yakin da Isra’ila ke yi mata ne da kananan yara.

Ofishin ya wallafa alkaluman a cikin wani rahoto mai shafuka 32 wanda ya kunshi watanni shida na ta’asar da Isra’ila ke aikatawa a zirin daga watan Nuwamba 2023 zuwa Afrilu 2024.

Rahoton ya ce kimanin kashi 80 cikin 100 na wadanda abin ya shafa an kashe su ne a gidaje, sai kuma kashi 44 cikin dari wadanda yara ne da kashi 26 cikin 100 mata.

Galibin wadanda aka tabbatar sun mutu a Gaza kananan yara ne da ke tsakanin shekaru biyar zuwa tara.

Rahoton ya ce mafi karancin shekarun yaran aka kashe yaro ne mai kwana daya, kuma mafi girma mace ce mai shekaru 97.

Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce ci gaba da kai wadannan hare-hare da Isra’ila ke yi “yana nuna halin ko in kula ga mutuwar fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments