Biden Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya taya Donald Trump murnar lashe zabe ta wayar tarho kamar yadda Fadar White House ta tabbatar. Biden ya bayyana cewa

Shugaban Amurka Joe Biden ya taya Donald Trump murnar lashe zabe ta wayar tarho kamar yadda Fadar White House ta tabbatar.

Biden ya bayyana cewa zai tabbatar da ya mika mulki cikin sauƙi, ya kuma gayyaci Trump zuwa Fadar White House domin su tattauna.

Zai kuma yi jawabi ga ’yan kasar ranar Alhamis kan sakamakon zaɓen da kuma shirin miƙa mulki, cewar sanarwar.

Biden ya kuma yi wa Kamala murnar kammala yakin neman zaɓenta mai cike da tarihi.

Wannan zuwa ne bayan da ’yar takarar jam’iyyar Democrats, Kamala Harris, ta amince da shan kaye a zaɓen da aka gudanar a ranar Talata.

Kamala Harris wadda ita ce Mataimakiyar Shugaba Biden, ta kira Donald Trump a wayar tarho domin taya shi murnar lashe zaɓen shugaban kasa, a cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta CBS.

A yayin kiran ne kum Kamala ta jaddada batun mika mulki cikin lumana, da kuma zama shugaba na kowa da kowa ga Amurkawa, kamar yadda wani mai taimaka mata ya faɗa wa CBS.

Kazalika, kungiyar yakin neman zaben Trump ta fitar da sanarwa bayan Kamala Harris ta yi magana da shi inda ta amince da shan kayen.

Steven Cheung, darektan sadarwa na yakin neman zaben, ya ce Trump ya jinjina wa “jarumtar Harris, kwarewa, da jajircewa a lokacin yakin neman zaɓe da kuma bayansa, kuma shugabannin biyu sun amince kan muhimmancin haɗa kan kasar.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments