A yau Talata ne Rasha ta harba taurarin dan’adam din guda biyu kirar Iran da su ne, “Kausar” da kuma “ Huda-huda”.
Taurarin dan’adam din na Iran da aka kera a cikin gida, an harba su ne da na’urar Rasha wacce a lokaci daya take iya harba taurarin dan’adam 53, zuwa sararin samaniya.
Za a yi amfani da taurarin dan’adam din ne domin gudanar da bincike a fagagen muhalli,albarkatun karkashin kasa da kuma ayyukan agaji alokacin da ake fuskantar ibtila’i na dabi’a.
Tauraron dan’adam na “Kausar’ yana da nauyin kilo 30, kuma shi ne wanda zai yi aiki a fagen noma da daukar taswirar kasa daga sama. Zai kuma dauki shekaru 3.5 yana iyo a sararin samaniya da nisan kilo mita 500 daga kasa.
A cikin shekarun bayan nan Iran tana harba taurarin dan’adam a nan cikin gida da kuma amfani da na’urorin Rasha da cibiyarta ta Khazakistan.