A Jamus, kyamar Musulmi na dada karuwa a kasar.
A wani rahoto da aka fitar a cikin watanni tara na shekarar 2024, hukumomin ‘yan sanda a Jamus sun ce mutane 42 da suka jikkata, ciki har da hudu masu tsanani, a duk fadin kasar, na da nasaba ne da kyamar Musulunci.
Sai dai wadannan alkaluma ba su da tabbas, domin a wasu lokuta ba a kai rahoton aikata laifuka kai tsaye ko kuma a lokacin bincike ne kawai ake gano dalilan dake da alaka da kyamar Musulunci.
A cikin rubu’i na uku na wannan shekara, an samu rahotannin laifuka 117, wanda ya nuna an samu raguwa idan aka kwatanta da kashi na biyu, inda aka samu laifuka 139.