Wani Harin Isra’ila Ya Yi Ajalin Falasdinawa 77 A Beit Lahaya Dake Arewacin Gaza

Jiragen yakin kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani gini da Falasdinawa ke fakewa a arewacin zirin Gaza, inda suka kashe mutane da dama

Jiragen yakin kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani gini da Falasdinawa ke fakewa a arewacin zirin Gaza, inda suka kashe mutane da dama tare da kama wasu da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, akalla fararen hula 77 da suka hada da mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu a harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani bene mai hawa biyar da ke birnin Beit Lahaya a ranar Talata.

Rahotanni sun ce mutane da dama na makale a karkashin baraguzan ginin yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da aikin gano wadanda suka tsira.

A halin da ake ciki, daraktan asibitin Kamal Adwan, ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa da dama daga cikin wadanda suka jikkata na iya mutuwa saboda karancin kayan aiki.

Ya kara da cewa “Dole ne duniya ta dauki mataki ba wai kawai kallon kisan kiyashin da ake yi a zirin Gaza ba.”

“Muna kira ga duniya da ta aiko da tawagogin likitoci na musamman don kula da mutane da dama da suka jikkata a asibiti.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments