Makayan na Hizbullah sun sanar da cewa, sun kai hari akan sojojin mamaya dake kusa da “Babu Fatima” wanda ke yankin Kafar-Kila, haka nan kuma a Aytarun.
Hare-haren na kungiyar Hizbullah sun yi sanadiyyar jikkata da kashe sojojin mamaya.
Bugu da kari, mayakan na Hizbullah sun harba makamai masu linzami a cikin Falasdinu dake karkashin mamaya ta hanyar harba makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki.
Wasu daga cikin wuraren da mayakan na Hizbullah su ka kai wa hari a yau Litinin da akwai, Nahariya inda su ka harba makamai masu linzami 15.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa 5 daga cikin sojojinsu sun halaka a fadan da suke yi da mayakan kungiyar Hizbullah a kudancin Lebanon daga cikinsu da akwai wasu manyan jami’ai.
Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma ambaci cewa a jiya Lahadi ne aka kashe wadannan sojojin 5 daga cikinsu har da malamin addini; Rabi Avi Goldbirag wanda yake yi wa sojoji wa’azi, sannan kuma ya shiga yaki.
Dama a jiya Lahadi ne dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wani “cliff” da take nuna harin da ya kai wa sojojin mamaya a kusa da garin Dhaibah da kuma Rub-Salasin. A jiya Lahadi kungiyar ta Hizbullah ta kai wasu hare-haren da jirage marasa matuki barin sojan HKI na “Ibl al-qamh”, sai kuma sansanonin soja na “Iliat Hashahir” da kuma Nahariya.