Pakitsan: Isra’ila Barazana Ce Ga Zaman Lafiya Da Tsaron Yanki Da Duniya

Kakakin majalisar kasar Pakistan Sardar Ayaz Sadiq ya bayyana cewa; Kasarsa tana yin tir da harin da Isra’ila ta kai wa Iran, kuma yana cin

Kakakin majalisar kasar Pakistan Sardar Ayaz Sadiq ya bayyana cewa; Kasarsa tana yin tir da harin da Isra’ila ta kai wa Iran, kuma yana cin karo da dokokin kasa da kasa.

Kakakin  Majalisar dokokin kasar ta Pakistan ya kuma ce; Cigaba kai wa kasashe hare-hare da Isra’ila take yi, yana a matsayin barazana ga zaman lafiya na wannan yankin da kuma duniya.”

Har ila yau kakakin majalisar dokokin kasar ta Pakistan ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma MDD da su dauki matakin da ya dace domin magance wannan matsalar.

Jami’an gwamnatin Pakistan da su ka hada da fira minista Shabbaz Sharif sun nuna goyon bayansu ga Iran tare da yin tir da harin da HKI ta kawo ma ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments