Kungiyar Hizbullah ta sanar da kaddamar da wani hari ta sama a sansanin jiragen sama na Tel Nof da ke kudancin Tel Aviv tare da wasu sojoji masu kula jiragen yaki marasa matuka na Isra’ila, inda aka kai musu hari kai tsaye.
Hezbollah ta kan sanar da kai hari kan cibiyoyin sojin Isra’ila amma sanarwar da ta bayar a wannan Asabar cewa ta kai harin ta sama da jirage marasa matuka kan sansanin Tel Nof shi ne irinsa na farko cikin shekara guda.
Har ila yau, ta harba makamin roka kan sojojin Isra’ila da ke kusa da wani kauye a kudancin kasar Lebanon, inda sojojin Isra’ila suka shafe makonni suna kokarin kutsawa cikin kasar.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce mayakanta sun harba makami mai linzami kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke wajen kauyen Aita al-Shaab, inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun Hizbullah da sojojin yahudawan Isra’ila cikin makonni biyu a jere.
An yi ta jin karar harbe-harbe a arewacin yankunan Falasdinawa da yahudawa suka mamaye saboda kutsawa da jiragen sama marasa matuka da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta harba zuwa wadannan yankuna.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Hizbullah ta bayyana a takaice cewa mayakanta sun kai hari a matsugunan Kiryat Shmona da makamin roka.