Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, fira minisa Netenyahu da ministansa na yaki Yoav Gallent sun buya a wani wuri na karkashin kasa a ma’aikatar yaki.
Netenyahu da ministan nasa na yaki sun buya ne a saboda tsoron harbo makamai daga Lebanon da sauran ‘yan gwgawarmaya.
Bugu da kari, jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra’ila, sun buya ne a daidai lokacin da sojojinsu suke kawo wa Iran hari.
Da misalin karfe 2: 15 na daren jiya ne Asabar ne dai aka ji kara mai karfi a yammacin birnin Tehran, wanda daga baya ta bayyana cewa, yana da alaka de da yadda makaman Iran suke kakkabo hare-haren da HKI ta kawo a wasu sassa na babban birnin kasar.
Sai dai makaman tsaro sararin samaniya sun yi nasarar kakkabo makaman na HKI.
Wata majiyar ta tabbatar da cewa, babu wani jirgin saman HKI na yaki da ya shigo sararin samaniyar Iran, sun harbo makaman ne daga wajen kasar kamar yadda kamfanin dilllacin labarun “Tsanim” ya ambata.
Kamfanin dillancin labarun “Tasnim” ya kuma ce, tabbas HKI za ta fuskanci mayar da martanin harin da ta kawo.
.