Wasu daga cikin hotunan da jami’an leken asiri na sojin Isra’ila suka amince a buga a wannan Talata, game da harin da Hizbullah ta kai a kan gidan Benjamin Netanyahu, sun nuna barna a wata taga mai dakuna da daya daga cikin jerin hare-haren da Hizbullah ta gudanar a ranar Asabar.
Wasu daga cikin tashoshin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka watsa hotunan, duk kuwa da Isra’ila ta hana dukkanin kafofin yada labaranta daukar hotunan wurin da kuma watsa su.
Wannan yana zuwa nea daidai lokacin da kungiyar Hizbullah ta samara hukuamncea kan cewa ita ce ta kaddamar da hari kan gidan Netanyahu.
Da dama daga cikin yahudawan sahyuniya masu sharhi kan harkokin siyasa da tsaro, sun yi imanin cewa, harin na Hizbullah ya zubar da tinkahon Isra’ila na nuna fifiko ta fuskar tsaro a dukkanin fadin gabas ta tsakiya.