Hamas Ta Tabbatar Da Shahadar Shugabanta Yahya Sinwar

A yau Juma’a ne shugaban kungiyar ta Hamas a yankin Gaza, Khalilul Hayyah, ya gabatar da jawabin alhinin shahadar Yahya Sinwar,tare da bayyana cewa ya

A yau Juma’a ne shugaban kungiyar ta Hamas a yankin Gaza, Khalilul Hayyah, ya gabatar da jawabin alhinin shahadar Yahya Sinwar,tare da bayyana cewa ya yi shahada ne yana gabata a filin daga ba mai juya baya ba.

Khalilul Hayyah ya kuma ce; Hamas tana mika ta’aziyyarta ta sha’adar jarumi, gwarzo, wanda ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa saboda Falasdinu, ya gabatar da ruhinsa a jihadi saboda Allah da ‘yanto da kudus,ga al’ummarmu baki daya, da dukkanin ‘yantattu a duniya.

Khalilul Hayya, ya kuma bayyana Shahid Yahya Sinwar da cewa, mutum ne wanda ya gaskata Allah, don haka Allah ya zabe shi a matsayin shahidi tare da wadanda su ka gabace shi,’yan’uwansa shahidai.

Shugaban kungiyar ta Hamas a yankin Gaza, ya kuma kara da cewa,kungiyar za ta cigaba da tafiya akan tafarkin shugabanninta shahidai, wadanda su ka share hanya, za kuma su cigaba da tsayin daka har zuwa lokacin ‘yanto da Falasdinu da kafa ‘yantacciyar Falasdinu.

A jiya Alhamis ne dai HKI ta sanar da kashe Yahya Sinwar a harin da take kai wa a yankin Gaza ba tare da ta san cewa shi ne ba.

Sai dai sojojin sun ce, bayan yin gwaji DNA sun tabbatar da cewa jagoran Hamas ne su ka kashe.

Sinwar ya yi shahada yana dauke da bindigar da yake harbin sojojin mamaya da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments