Hizbullah: Karfinmu Yana Nan Daram

A wani faifan bidiyo da dakarun kungiyar Hizbullah su ka fitar a jiya Litinin,sun nuna jirage marasa matuki da suke da su,da kuma wasu makamai,

A wani faifan bidiyo da dakarun kungiyar Hizbullah su ka fitar a jiya Litinin,sun nuna jirage marasa matuki da suke da su,da kuma wasu makamai, sannan su ka karkare da cewa; Karfinmu yana nan daram.

Fitar da wannan faifan bidiyo din ya zo ne domin rusa farfagandar da ‘yan sahayoniya suke yi  na cewa sun rusa mafi yawancin makaman kungiyar Hizbullahi,kuma kwana daya bayan harin da kungiyar ta kai akan wani boyayyen sansanin sojan HKI a garin Haifa. Sojojin mamaya da dama ne su ka halaka, wasu kuma su ka jikkata.

Wasu daga cikin jirage marasa matukin da aka nuna suna dauke da makamai masu linzami da suke cikin shirin harbawa.

Bugu da kari a jikin bangon rumbun ajiyar jiragen marasa matuki an manna hoton shahid Sayyid Hassan Nasrallah.

A gefe daya kungiyar ta Hizbullah ta yi watsi da wata Farfagandar da sojojin HKI suke yi na nuna fayafayen bidiyo na shiga cikin wasu garuruwa na Kudancin Lebanon, tare da cewa, ana yin fada da su ne akan iyaka.

Wata sanarwar da ta fito daga kungiyar Hizbullah ya ambaci cewa mayakansu sun kakkabo jirgin sama na leken asiri mallakin HKI samfurin “Hermes 450”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments