TATTAUNAWA: Dalilin da ya sa babu maganin rigakafin cutar ƙyanda ‘Mopox’ na yara a Najeriya – Jami’in UNICEF

PREMIUM-Shugaban fannin lafiyar jama’a na UNICEF Eduardo Celades a hira da ya yi da PREMIUM TIMES ya yi karin haske kan yaduwar cutar ƙyanda ‘Mopox’,

Dalilin da ya sa babu maganin rigakafin cutar ƙyanda ‘Mopox’ na yara a Najeriya – Jami’in UNICEF

PREMIUM-Shugaban fannin lafiyar jama’a na UNICEF Eduardo Celades a hira da ya yi da PREMIUM TIMES ya yi karin haske kan yaduwar cutar ƙyanda ‘Mopox’, rashin samun maganin rigakafin cutar da sauran matsalolin da fannin Kiwon lafiyar Najeriya ke fama da su.

PT: Yaya yara kanana suka zama cikin rukunin mutanen da suka fi kamuwa da cutar?

Celades: Da farko kamata ya yi mu fahimci yadda cutar ke yaduwa domin Mpox cuta ce da ake iya kamuwa da ita idan ana yawan cudanya da wadanda ke dauke da cutar.

Ana iya kamuwa da cutar idan aka gogi zufan jikin wanda ke dauke da cutar, idan ruwan kurarrajin jikin wanda ke dauke da cutar ya taba jikin mutum, idan mutum ya kwanta a inda mai fama da cutar ya kwanta duk ana iya kamuwa.

Mu da dake UNICEF mun lura cewa cutar ya fi yaduwa a cikin gida sannan yara kanana na daga cikin rukunin mutanen da suka fi saurin kamuwa da cutar musamman idan yaro bashi cikin koshin lafiya.

A duniya kashi 65% daga cikin wadanda suka kamu da cutar yara ne ‘yan kasa da shekara biyar sannan a Najeriya daga cikin mutum 67 din da suka kamu 24 yara ne ‘yan kasa da shekara 10.

PT: A kwanakin baya gwamnatin Najeriya ta samu tallafin maganin rigakafin cutar guda nawa ne na yara a ciki?

Celades: Tabas Najeriya ta karbi kwalabe 10,000 na maganin rigakafin cutar amma babu na yara a ciki. Maganin na mutanen da suka dara shekaru 18 ne.

PT: Me ya sa hakan ke faruwa?

Celades: A yanzu haka Kamfanoni uku ne ke hada maganin rigakafin cutar inda daya na Japan, Amurka da Denmark.

Maganin rigakafin da Amurka da Denmark suke yi ba za a iya amfani da su wa yara ba sannan wanda Japan ke yi na yara ƴan asalin ƙasar ne.

Gwamnati za ta yi amfani da maganin rigakafin cutar kwalabe 10,000 din da ta samu wa mutanen da suka yi awa 42 bayan cudanya da wadanda suka kamu da cutar.

A lissafe dai mutum 5,000 ko Kasa da haka ne kadai zai su amfana da maganin saboda kwalabe 10,000 ne kawai ake da su sannan ma daga ciki akan samu wadanda suka lalace.

A dalilin haka yake da mahimmanci wajen kiyaye sharudan guje wa kamuwa da cutar, yi wa mutane gwajin cutar da gudanar da bincike domin gano wadanda suka kamu da cutar.

PT: Menene dalilin rashin samun maganin rigakafin?

Celades: Dalilin da ya sa ake fama da karancin maganin rigakafin shine saboda karancin Kamfanonin hada maganin sannan Kuma cutar sabuwar cuta ce da ba a yawan kamuwa da ita ba a baya.

A dalilin haka ya sa Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO, UNICEF da CDC Afrika ke kira ga kasashen duniya da su rika tallafawa wa kasashen da suka fi fama da cutar da maganin rigakafin.

Najeriya ita ce kasa ta farko a Afrika da ta samu tallafin maganin rigakafin. Daga ita sai Jamhuriyar Kongo DRC.

PT: Wasu matakai ne aka dauka domin kula da kare yara wajen kamuwa da cutar?

Celades: Matakin da muka dauka shine killace yaran da suka kamu da cutar, gudanar da bincike domin gano wadanda suka yi cudanya da su domin yi musu allurar rigakafi idan manya ne sannan idan yara ne suma a killace su sannan da jadadda mahimmancin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar.

PT: Yanzu da Kasa ke fama da karancin maganin rigakafi wani mataki za ka shawarce mutane su dauka domin gujewa kamuwa da cutar?

Celades: Mopox cuta ce dake da nau’ika biyu Celades I da Celades II kuma ma CladesI ya rabu zuwa Celades IB.

Afrika ta Tsakiya na fama da yaduwar Mopox nauyin Celades 1 wanda ya fi kisan mutane sannan Afrika ta Yamma na fama da Celades II.

A Najeriya Clades II ne ake fama da shi. duk da haka kamata ya yi kasan ta mike

Gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da ake zargin an kamu da cutar, an yi cudanya da wanda ke dauke da cutar ko an ga alamun cutar a jiki da killace kai domin guje wa yada cutar.

Alamun cutar sun hada da ciwon kai, zazzabi, fesowar kurarraji masu zafi da sauran su.

PT: Wani mataki ne kuka dauka don gano cutar musamman yadda CDC Afrika ke nuniya da rashin iya gano cutar wasu lokuta idan an yi wa mutum gwajin cutar?

Celades: Hakan na faruwa amma duk Matakin gano cutar da aka dauka kamata yayin a karfafashi.

Zuwa yanzu UNICEF ta shigo da kayan gwajin cutar 2,000 da kasar Amurka ta tallafa wa Najeriya da su sannan ya zama dole a rika sa ido da gudanar da bincike musamman a sansanoni ‘yan gudun hijira domin gano bullowar cutar.

PT: Kana da rahotan bullowar cutar a sansanin ‘yan gudun hijira?

Celades: A yanzu haka bani da labari amma kamata yayin a mai da hankali kan rukunin mutanen da suka fi kamuwa da cutar.

Wadannan rukunin mutanen sun hada da jami’an lafiya, mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira, gidajen yari da yara kananan musamman wadanda basu da koshin lafiya.

PT: Kana da labarin bullowar zazzabin cizon sauron da baya jin magani a Najeriya?

Celades: A yanzu haka bani da labari amma ina da masaniyar cewa akwai wasu kasashen dake makwabtaka da Najeriya dake fama da wannan matsala wanda ya kamata Najeriya ta dauki matakan yakar cutar.

A cikin wannan shekarar Najeriya ta hada maganin zazzabin cizon sauro wanda WHO ta amince da ingancinsa.

A gani na wannan babban ci gaba ne kasar ta samu domin maganin zai taimaka wajen yakar cutar a farashi mai sauki.

PT: Menene ya sa zazzabin cizon sauro baya jin magani?

Celades: Babban matsalar dake sa cutar rashin Jin magani shine yadda mutane ke Shan magunguna ba tare da izinin likita ba.

Wannan matsala na faruwa da wasu cututtuka ba zazzabin cizon sauro ba kadai.

Tsananta yin gwajin cutar da bada maganin cutar a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin matakan da za su taimaka wajen kawar da matsalar.

PT: Wasu matsaloli ne ke hana Najeriya rage yawan mace-macen yara kanana da mata?

Celades: Akwai matsaloli da dama dake hana Najeriya wajen rage yawan mace-macen yara kanana da mata.

Wadannan matsaloli kuwa sun hada da rashin iya zuwa asibiti wanda ka iya faruwa a dalilin talauci, nisan asibiti.

Bincike ya nuna cewa mata masu ciki kashi 70% ke zuwa awo a asibiti akalla sau daya, kashi 60% na zuwa awo akalla sau hudu sannan kashi 50% na haihuwa tare da taimakon kwararrun jami’an lafiya.

Muna sa ran cewa aiki da matakan inganta fannin lafiya da wannan gwamnati da ministan lafiya suka dauko za su taimaka wajen cin ma burin samar da kiwon lafiya ga kowa da kowa.

PT: Wasu matakai ne UNICEF ta dauka domin inganta lafiyar yara a birane da karkara?

Celades: UNICEF na samun yara a birane da basu yin allurar rigakafi a Najeriya inda a dalilin haka za ta yi amfani da yanar gizo domin wayar da kan mutane mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi.

UNICEF ta Kuma tsaro matakai iri-iri da za su taimaka wajen wayar da kan mutane mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi a kananan hukumomi a kasar nan.

PT: Ta yaya UNICEF ke hada hannu da kananan hukumomi wajen inganta lafiyar mutane a Najeriya?

Celades: UNICEF ta tsara shiri na hada hannu da mutane domin inganta lafiya a kasar nan.

A dalilin shirin UNICEF na aiki da mutum 16,000 inda da dama daga cikin mata ne dake taimakawa wajwn wayar da kan mitane mahimmancin yin allurar rigakafi da sauran hanyoyin inganta lafiya.

UNICEF na kuma na inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin kasar.

PT: Wasu bangarori ne kake ganin ya kamata gwamnati ta mai da hankali a kai domin inganta lafiyar yara kanana a Najeriya?

Celades: Bangarori lafiyar da ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai sun haɗa inganta cibiyoyin kiwon lafiya, inganta yin wa yara allurar rigakafi da ware isassun kudade domin inganta fannin lafiya gaba daya.

UNICEF na kuma goyan bayan kokarin da gwamnati ke yi wajen samar da magungunan rigakafi a kasar nan domin a shekarar da ya gabata gwamnati ta shigo da maganin rigakafin Rotavirus, yanzu ta shigo da maganin HPV domin kare mata daga cutar daji sannan da maganin PVC dake kare yara daga kamuwa da cutar sanyin dake kama hakarkari ‘Pneumonia’.

Shekara mai zuwa gwamnati za ta shigo da maganin rigakafin kare yara daga kamuwa da cutar Bakon dauro.

UNICEF na sa ran cewa a dalilin matakan da wannan gwamnati ta dauka za a samu ci gaba a fannin kiwon lafiya musamman wajen kula da yara nan da shekaru uku masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments