Sharhin Bayan Labarai Kan Ci Gaba Da Gwagwarmayar Falasdinawa

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan sanarwar da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka fitar ne cewa: Bayan shekara guda fara kaddamar da hare-haren

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan sanarwar da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka fitar ne cewa: Bayan shekara guda fara kaddamar da hare-haren zalunci kan Gaza, har yanzu ‘yan gwagwarmaya suna ci gaba da kalubalantar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, da ni Sunusi Wunti zan jagoranci gabatar muku da shirin kamar haka:-

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna cigaba da gwabza kazamin fada da sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza, lamarin da ke ci gaba da janyo hasarar rayuka da na dukiya a tsakanin bangarorin biyu. A yayin da dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas suka sanar da aiwatar da hare-haren soji kan sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ke kutsawa cikin shiyar arewacin Zirin Gaza, kamar yadda dakarun Sarayal-Quds bangaren sojin kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami sun watsa hotunan harin da suka kai wa wani tankar yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a tsakiyar sansanin Jabaliya. Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi furuci da halakar wani Sajan su guda, da kuma wani mummunan rauni da aka yi wa wani soja na daban a arewacin Zirin Gaza.

Nasara tana ci gaba da samuwa ga al’ummar da ake neman murkushe ta. Wannan shi ne halin da bangarorin gwagwarmayar Falasdinawa ke ciki a Zirin Gaza, bayan tsawon shekara guda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kaddamar munanan hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Falasdinawa da kuma kokarin kutsawa ta kasa kan duk wani yankin Falasdinawa domin ganin ta murkushe Falasdinawa musamman ‘yan gwagwarmayarta domin samun damar shimfida bakar siyasarta ta wuce gona da iri da babakere. Har yanzu haka dai gwagwarmayar Falasdinawa na ci gaba da fuskantar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a dukkan fagagen fama.

Yankin arewacin Zirin Gaza shi ne yankin da ya fi tsananin dauki ba dadi tsakanin ‘yan gwagwarmaya da sojojiin mamaya a ‘yan kwanakin nan, yayin da dakarun Izzuddeen Al-Qassam suka kai farmakin soji kan sojojin mamaya da suka kutsa cikin sansanin Jabaliya da sauran yankunan.

‘Yan gwagwarmaya suna ci gaba da gwabza kazamin fada daga nesa da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yin kutse a shiyar yammacin sansanin Jabaliya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkata a tsakanin sojojin ‘yan mamaya. Haka zalika mayakan Izzuddeen Al-Qassam sun tarwatsa wata mota da take dauke da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila tare da yin arangama da wata runduna ta musamman ta sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda suka kashe tare da raunata sojojin masu yawa a wannan yanki.

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun kuma yi ruwan bama-bamai da harsasai kan hedkwatar rundunar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin hukumar farar hula a gabashin sansanin Jabaliya a shiyar arewacin Zirin Gaza.

A wani farmaki na musamman da dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas suka kai kan tawagar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka kunshi sojoji goma da makami mai linzami sun kashe tare da raunata wasu daga cikinsu a shiyar arewacin birnin Gaza, kamar yadda dakarun gwagwarmayar suka harba makami mai linzami kan wata tawagar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila.

A nata bangaren, dakarun Sarayal -Quds bangaren sojin kungiyar Harkar Musulunci ta Jihadul- Islami, sun yada hotunan wani tankin Merkava na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka tarwatsa shi da makami mai linzami na Tandom a lokacin da yake kutsawa cikin yankin Al-Qasasib da ke tsakiyar sansanin Jabaliya a yankin arewacin Zirin Gaza.

A nata bangaren, rundunar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta ikrarin halakar sojanta guda tare da wani na daban da yake cikin halin rai kwaikwai mutu kwaikwai sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Dangane da fadan da ake gwabzawa a tsakiyar Zirin Gaza, dakarun na Quds tare da hadin gwiwar dakarun Al-Nasir Salahuddeen sun yi ruwan bama-bamai kan hedikwatar sojojin mamaya na Juhr al-Dik.

Kamar yadda dakarun Shahid Abu Ali Mustafa tare da hadin gwiwar dakarun Al-Nasir Salahuddeen suka yi luguden wuta kan tungar sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ke cikin yankin ‘Netzarim’.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments