Wani Balarabe Mai Dauke Da Passpo Din HKI Ya Kai Hari Akan Sojojin HKI

Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa, a yau Lahadi wani Bafalasdine ya kai hari a yankin “Bi’iri –Saba’a” inda ya kashe soja mace

Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa, a yau Lahadi wani Bafalasdine ya kai hari a yankin “Bi’iri –Saba’a” inda ya kashe soja mace daya da kuma jikkata wasu sojojin 13.

Kafar watsa labarun HKI ta kuma kara da cewa, maharin wanda tuni ya yi shahada, yana dauke da paspo din Isra’ila, ya kuma fito ne daga yankin Naqab dake kudancin Falasdinu dake karkashin mamaya.

Radiyon sojojin HKI ya ce, maharin ya kai wa sojar mace hari da wuka, sannan ya kwace bindigarta, wacce ya yi amfani da ita ya bude wuta akan sauran sojojin da suke wajen.

A gefe daya a yau Lahadi sojojin HKI sun sanar da cewa wani soja mai mukamin Manjo ya mutu sanadiyyar raunin da ya sau a wani fada da ‘yan gwagwarmaya a Gaza a watan Yuni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments