Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi wanda ya gabatar da jawabi a yau, ya bayyana cewa;Farmakin Guguwar Aqsa, ya sarfado da tunanin jihadi a tsakanin al’umma.
Bugu da kari Sayyid Abdulmalik al-husi ya ce; guguwar Aqsa ya kawo karshen akidar yakin HKI ta fara yaki da gama shi a cikin kwanakin kadan, maimakon hakan an tilasta musu yin yaki na tsawon lokaci.
Har ila yau Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce; Ba Falasdinu ne kadai HKI take da kwadayin shimfida iko a cikinta ba, tana son shimfida iko a dukkanin kasashen larabawa da ma wannan yankin.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce; Abinda HKI take yi a kasa shi ne babban dalili akan cewa tana son yin iko ne da dukkanin wannan yankin.
Haka nan kuma shugaban na kungiyar Ansarullah ta Yemen ya ce; HKI tana son ganin ita ce kasar da ta fi karfin soja a gabas ta tsakiya da zai ba ta damar mamaye wannan yankin.