Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya caccaki shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan kiran da ya yi na kawo karshen bai wa haramtacciyar kasar Yahudu makamai, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyar Hizbullah da Iran.
A wata hira da ya yi da kafofin yada labaran Faransa da aka watsa a wannan Asabar, Macron ya yi kira da a samar da mafita ta siyasa kan rikicin yankin gabas ta tsakiya, ya kuma ce ya kamata kasashen yammacin duniya su daina kai makaman yaki a Gaza.
Ya kira ci gaba da tashin hankalin a matsayin babban kuskure, kuma ya yi gargadi game da mayar da Lebanon zuwa wata “sabuwar Gaza.”
Netanyahu ya mayar da martani a wata sanarwa mai zafi a kan dandalin X , inda yake magana da Macron kai tsaye.
Ya ce Isra’ila tana yaki ne a bangarori bakwai da abokan gaba masu wayau, in ji shi, yayin da yake magana game da rikice-rikicen da Isra’ila ke yi da Hamas, Hizbullah, Houthis, da kuma Iran gami da kawayenta a Siriya da Iraki.
Netanyahu ya ce”Ya kamata dukkan kasashen da ke da wayewa su tsaya kyam a bangaren Isra’ila.” Yana mai cewa kalaman Macron dangane yakin Isra’ila da kuma yin kirada a daina bata makamai babban abin kunya ne.