Iran: Isra’ila ba ta cancanci zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta cancanci zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya, Biyo bayan

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta cancanci zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya, Biyo bayan hare-haren kisan kiyashin da ta kaddamar kan Gaza da Lebanon.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya bayyana hakan ne a wannan Alhamis a birnin New York na kasar Amurka, yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD, kan halin da ake ciki a yankin, wanda ya mayar da hankali kan batun kasar Lebanon.

Taron dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza, da kuma kara munanan hare-hare kan kasar Labanon.

Hare-haren kan Lebanon sun biyo bayan kaddamar da hare-haren wuce gona da iri da sojoji ke kaiwa ne kan Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya yi sanadin shahadar dunban fararen hula akasarinsu mata da kananan yara.

Araghchi ya ce “A ci gaba da ta’asar da Isra’ila take yi a Falasdinu da ta mamaye, a yanzu tana kaddamar da yaki na wuce gona da iri kan kasar Labanon tare da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kan iyaka da kuma cikin kasar.”

Ya bayar da misali da yadda ta yi ta tarwatsa dubban na’urorin sadarwa ranakun 18 da 19 ga watan Satumba, inda suka kashe akalla mutane 39 tare da raunata wasu sama da 3,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments