Hezbollah ta harba manyan makamai da dama a kan sansanin sojin Isra’ila da ke Haifa

Kungiyar Hizbullah ta harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye,  wanda ke zama daya daga

Kungiyar Hizbullah ta harba manyan makaman roka daga Kudancin Lebanon zuwa yankunan da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye,  wanda ke zama daya daga cikin hare-haren rokoki mafi muni da Isra’ila ta gani tun daga lokacin da ta kaddamar da yaki kan Gaza.

An yi ta jin karar harbe-harbe a yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, wanda ke da nisan kilomita 40 daga gabashin Falasdinu da aka mamaye zuwa yankunan arewacin Jenin a yammacin gabar kogin Jordan. Wasu daga cikin matsugunan da aka ji karar sautin harbe-harben suna da nisan kusan kilomita 60 daga layin da aka shata bayan janyewar Isra’ila daga Lebanon.

Kungiyar gwagwarmayar – Hezbollah, ta kai hare-hare sau uku a safiyar wannan Lahadi, a kan yankunan Falasdinawa da ke karkashin mamayar Isra’ila, a matsayin martani ga kisan kiyashin da “Isra’ila” ta yi a cikin makon da ya gabata kan fararen hula na Lebanon.

Farmakin farko kungiyar ta kaddamar da shi ne a kan sansanin sojin Isra’ila da ke Ramat David, da wani sansanin sojin sama na Isra’ila, inda kungiyar ta yi amfani rokoki samfurin Fadi 1 da Fadi 2, Har ila yau, ta kaddamar da farmaki na uku a kan wani

rukunin masana’antu na soja na Rafael da karfe 6:30 na safiyar wannan Lahadi, wanda kuma a wurin ne ake samar da kayan lantarki na Isra’ila, wanda yake a arewacin birnin Haifa.

Hizbullah ta tabbatar da cewa, wadannan hare-hare na goyon bayan al’ummar Palastinu masu tsayin daka a zirin Gaza ne, da kuma goyon bayan gwagwarmayarsu, da kuma wani bangare na martanin farko kan kisan gillar da yahudawan suka yi a yankuna daban-daban na kasar Labanon, a ranakun Talata da Laraba, lokacin da suka tarwatsa dubban na’urorin sadarwa Pagers da kuma na’urorin sadarwa, wanda aka fi sani da walkie-talkies ko kuma oba-oba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments