Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah Azzahra (s) 41

41-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

41-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya inda muka fara kawo maku hadisai wadanda suka yi Magana dangane da wafatin manzon All..(s) da kuma yadda ya yi kuka mai yawa saboda abinda zai faru da iyalan gidansa a bayansa.

Kuma ya tara Fatima da mijinta da yayanta Alhassan da Alhussain(a), a lokacin wafatinsa ya taratu, ya kuma yi wasiyyarsa ga Aliyu dan Abitalib (s) a gaban mala’iku sannan ya kafasu shaida a kan cewa ya mikawa Aliyu littafin wasiyyansa. Sannan ya koma ga Ubangijinsa a dai dai lokacinda kansa ya na kan kirjin Aliyu (a) sannan diyarsa Zahra (s) da yayanta Alhassan da Alhussain suna kuka a gewayensa.

Tun daga lokacin bakinci da bacin rai suka shiga zuciyar Zahra (s), tana kuka fiye da kowa, tana rera kisisdu na makokin mahaifinta.

Mun san yayan mata sukan yi kokan iyayensu a duk lokacinda irin wannan musiba ta rasuwar iyayensu ya samesu. Amma dangane da Zahra(s) wafatin manzon All..(s) a wajenta ya fi wafatin mahaifi ko babanta. Don dangantaka tsakaninta da mahaifinta ya fi na dabi’a, mun yi magana dangane da wannan a baya. Ita ta rasa wanda ya san matsayinta a wajen All..T, ta rabu da wanda ya san cewa ita ce Maryam babba, kuma itace shugaban matan Aljanna, ta rabu da wanda ya san cewa ma’asuma ce bata kuskure, ta ranbu da wanda ya san tafsilin musibun da zasu fada mata bayan wafatinsa.

Ta na kuka don yankewar wahyi daga sauka a cikin dakinta ko gidanta. Tana kuka don sanin rabuwa da wanda ya san musibun da za su fada mata da kuma yayanta a bayanta kamar yadda mahaifinta ya shaida mata.

Bayan wafatin manzon All…(s) Zahra’u (a) ta kasa zama a gidanta, saboda yawan kuka, takan nisanci cikin gari, wani lokacin ta je Baki’a tana kallon kaburburar matattu musulmi, wani lokaci da Je Uhudu a wajen kabirin ammin babanta Hamza dan Abdulmuttalib(s). Wani lokaci ta je wajen kabarin babata, ta dauki kasar Kabarin tana sunsunawa, mai don jin kanshin mahaifinta manzon All..(s).

Saboda yawan kokanta, sai da mijinta Aliyu (a) ya gina mata runfa na kuka a wajen Madina kusa da makabartan baki tana zuwa can ko wace rana tare da yayanta tana kukan mahaifinta(s) don kada ta takurawa makobtanta da yawan kuka.

Wasu malamai sun bayyana cewa Zahra’u (s) bata dade bayan babanta ba sai na kwanaki 75 ta bashi, saboda bakinciki rabuwa da shi, da kuma saboda wasu al-amura marasa dadi da suka faru da ita bayan wafatin mahaifinta dangane da shugabancin mijinta a matsayin wasiyyin manzon All..(s).

Kafin mu karasa da abubuwan da suka faru da Fatimah (a) bayan wafatin mahaifinta manzon All..(s) bari mu koma bayan kadan don jin yadda aka yi jana’izar manzon All..(s).

Bayan da Aliyu (a) ya kammala wankan da kuma yiwa manzon All..(s) likkafani da sauran abubuwan da yakamata a yiwa mamaci, da farko yayai masa likkafani ni da kayakin Ihraminsa na aikin Hajjin da yayi tilo, kuma shi ne hajjin bankwana.

Sannan Aliyu(a) yayi masa kabari ne a dakin da ya rasu. A mazhabar iyalan gidan manzon All..(s), manzon All..(s) ya gina daki na musamman don wafatinsa cikin gidansa, ba karmar yadda wasu suke cewa ya yi wafati a dankin daya daga cikin matansa ba. Don haka a wannan dakin ya rasu a nan aka yi masa wanka a nan kuma aka yi masa sallah.

Banda haka sallar jana’izar manzon All..(s) ya bambanta da sauran musulmi. Kuma shi ne da kansa ya fadawa Aliyu dan Abitalib (a) yaddda za’a yi masa sallah. Ya ce masa, da farko shi Aliyu dan Abitalib (a) a matsayinsa na wasiyyinsa shi ya fara yi masa sallah shi kadai.

A lokacinda ya kammala sai sauran iyalan gidansa suka shigo suka yi masa sallah sannan sauran sahabban manzon All..(s).

A wannan sallar ta jana’izar manzon All..(s). babu limami, don Aliyu (s) yana fada manzon All..(s)  shugabane a raye da kuma bayan wafatinsa.

Don haka abinda ya faru a lokacin sallar Jana’izarsa shi ne, mutane kimani goma-goma suke shigowa su yi sahu guda, a bayan gawarsa mai tsarki su yi masa Sallah.

Sannan Aliyu (a) yana karanta masu abinsa zasu fada a addu’o’in da suke yi a sallar tasu. Idan sun kare sai wata tawaga ta shigo.

Manzon All..(s) ya yi wafata a ranar Litinin 28 ga watan Safar shekara ta 11 bayan Hijira da misalin lokacin walaha, ko dhuha, rana ta tashi amma bata yi zafi ba. Sannan Aliyu (s) shi ne ya sauko da gawarsa mai tsarki zuwa cikin kabarisa, nau’in Lahadu da aka yi masa.

Wannan ya faru a daren laraba wato kimani kwanaki 3 da wafatinsa (s). Sai dai abin bakin ciki ba dukkan sahabban manzon All..(s) da suke madina ne suka sami damar yi masa sallah ba. Saboda wanda ya karanta tarihin wafatin manzon All,,, (s) zai san cewa, yan sa’o’i da wafatinsa wasu sahabban suka fara jayayye kan wanda zai gaje shi a matsayin shugaban al-umma a bayan sa. Don haka wannan shirin shugabancin ya shagaltasu daga sallar Jana’izar manzon manzon All..(s).

Idan mun sake dawowa kan bakin cikin Zahra (s) bayan wafatin manzon All..(s), malaman tarihi sun bayyana cewa ba’a sake ganinta(s) tana murmushi ba har zuwa wafatinta ita ma kwamatin 75 bayan mahaifinta, ko watanni 2 da mokonni 2 bayan wafatin mahaifinta (s).

An karbo hadisi daga Mahmood dan Lubaid yana cewa yan kwanaki, bayan wafatin manzon All..(s) Fatima (s) ta kansace tana zuwa kabarin shahidan uhudu ta je, inda kabarin ammin babanta Hamza dan Abdulmuttalib (s ) tana kukan wafatin mahaifinta (a), sai Mahmood dan Lubaid ya ce wata rana na sameta tana kuka a kusa da kabarin Hamza dan Abdul muttalib (a), sai na jirata har ta sami nutsuwa sai na matso kusa da ita, na yi mata sallama ta amsa, sai nace mata ya ya shugaban mata, kin karya zuciyarta da wannan yawan kunan naki, sai tace:

Ya aba Amrin, ya cancanta gareni na yi kuka don rasa mafifin mahaifa, manzon All..(s).

Ya yawan shauki na ga manzon All..(s).  sannan ta rera waka tana cewa.

Idan wani mutum ya mutu, ambatonsa yakan karanta::::: Amma ambaton Babana bayan wafati, wallah- Ya karu.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa bayan wafatin manzon All…(s), Fatima (s) tayi kuka mai yawa har sai da makobtanta suka hanata koka, don bata yankewa, sai ta rika fita zuwa Uhudu, a lokacinda rashin lafiyarta ya yi tsanani sai ta kasa zuwa Uhudu, tana zuwa makabartan Baki’a don, nan ya fi kusa da gari, da kuma baitul Ahzan shi ma kusa da Baki’a tana kuka. Kamar yadda zamu kawo nan gaba.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alikum wa ramatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments