Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya ta ce ta dakatar da shirin fara karbar harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur ɗin da ake shigowa da su kasar daga ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), George Ene-Ita, ya faɗa cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa ya kamata ‘yan Najeriya su daina fargaba.
A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da saka harajin kan man fetur da dizel, wanda zai kara farashin man da ake saukewa a defo-defo, kuma daya daga cikin manufarta shi ne karfafa matatun mai na cikin gida.
Gwamnatin Najeriya ta tsara fara aiki da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamban nan, kafin matakin da NMDPRA ta sanar.
Duk da manufar karfafa matatun mai na cikin gida da harajin zai yi, zai kuma iya jawo hauhawar farashin a gidajen mai kasancewar har yanzu Najeriya na shigo da fetur mai yawa daga kasashen waje.