Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kuduri Mai Lambar 2231 Ya Riga Ya Kawo Karshe.
Rahotanni sun bayyana cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baqa’I ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da yayi dangane da wa’adin kuduri mai lamba 2231 yace, adawar da kasahen biyu masu kujerun dindindin na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya suka yi ga kasashen turai, ya nuna cewa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kasa yanke shawarar maido da kudurorin da aka soke.
Da yake Magana a wajen taron manema labarai na mako mako da yake yi Baqai ya kara da cewa kawo karshen kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 2231 a ranar 18 ga watan oktoba ya nuna cewa duk wasu abubuwa da kudurin yake dauke da su a hukumance yazo karshe.
Kakakin yace kasar iran taba da hadin kai kan yarjejeniyar har zuwa shekara ta 2019 kamar yadda rahoton mutane 15 ya bayyana na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, sai dai janyewar da Amurka tayi a shekara ta 2018 da kuma kasashen turai na biye ma Amurka ya lalala tsarin da aka yi kuma yasa basu yi aiki da wajibinsu ba.