Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya ce, “Za a samu zaman lafiya na gaskiya a yankin Gabas ta Tsakiya ne kawai idan an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa ka’idojin kasa da kasa da kuma hanyar da za ta maido da hakkokin masu hakki.”
A jawabin da ya yi na bikin cika shekaru 52 na nasarorin da larabawa suka samu a yakin watan Oktoban 1973, Sisi ya yi nuni da cewa, yin amfani da karfin tuwo domin aiwatar manufa ne ke haifar da tashin hankali, yayin da zaman lafiya da aka gina bisa adalci yana samar da daidaito na gaskiya da kuma dorewar zaman tare a tsakanin al’ummomi.”
Ya yi nuni da cewa, tsagaita bude wuta, musayar fursunoni da fursunoni, da sake gina Gaza, da kuma fara aiwatar da tsarin siyasa cikin lumana da zai kai ga kafa da kuma amincewa da kasar Falasdinu, hanya ce madaidaiciya ta tabbatar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda shi ne abin da dukkan mu ke fata. A cikin wani yanayi mai alaka da hakan, ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya bayyana cewa, Alkahira “ba tana kin amincewa da tura dakarun kasa da kasa a Gaza ba,” amma “tana karfafa gwiwar yin hakan ne karkashin kuduri na kwamitin sulhu na MDD.