Cuba Ta Amince Da Hakkin Iran Na Mallakar Shirin Makamashin Nukliyar Na Zaman Lafiya

Shugaban kasar Cuba Miguel Mario Díaz-Canel ya na goyon bayan JMI a cikin shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya. Kamfanin dillancin labaran IP na

Shugaban kasar Cuba Miguel Mario Díaz-Canel ya na goyon bayan JMI a cikin shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin ganawarsa da kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof wanda yake ziyarar aiki a kasar.

Labarin ya kara da cewa kasashen biyu wato Iran da Cuba sun dade suna fada da takunkuman tattalin arziki na kasar Amurka, don haka kasashen biyu suna aiki tare da neman mafita daga wadannan takunkuman zalunci.

Taron kasashen biyu dai na zuwa ne a dai-dai lokacinda ake tada jijiyoyin wuya a yankunan Asiya ta kudu da kuma yankin Laten America kan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasashen yankunan guda biyu.

Diaz- Canel ya yi tir da shishigin da Amurka take yi a cikin al-amuran cikin gida na JMI, ya kuma kara da cewa gwamnatin Amurka ta yi kuskure da ta fice daga yarjeniyar JCPO ta shirin Nukliyar kasar Iran a shekara ta 2018. Kuma hakkin JMI ta tashe makamashin uranium a cikin kasarta kamar yadda yarjeniyar NPT ta tanadar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments