Iran Da Qatar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin  Al’ummar Syria A Cikin  Sha’anin Kasar

Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su

Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati.

A jiya Laraba ne dai Muhammad Ridha Shaibani ya kai ziyara birnin Doha  inda ya gana da ministan na kasar ta Katar  Muhammad al-Khalifi domin yin shawara akan Syria.

Shaibani ya bayyana mahangar Iran akan Syria, da  ya kunshi ganin an shigar da kowane bangare na al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da kasar, ya kuma zama sun taka rawa wajen ayyana makomar kasar.

A nashi gefen ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi ya yi ishara da rawar da Iran take takawa a cikin wannan yankin da kuma tasirisnta, haka nan kuma ya bayyana wajabcin ci gaba ta tuntubar juna  domin musayar ra’ayi akan halin da kasar ta Syria take ciki.

Haka nan kuma bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments