Kakakin sojan Iran Birgediya Janar Abul Fadal Shekarci ya ce duk wata tsokana da Amurka za ta yi wa Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani daga sojojin Iran.
Birgediya janar Shekarci wanda yake mayar da martani ga maganganun bayan nan na shugaban kasar Amurka Donald Trump akan Iran, a kira shi da mai mafarkin tsaye, sannan ya ce; duk wata tsokana daga Washingto za ta fusakanci mayar da martani mai tsananin gaske daga sojojin Iran.
Birgediya janar Shekarci ya kuma ce;Sojojin na Iran suna sa ido da bin diddigin duk wani kai da komo na sojojin Amurka da ‘yan sahayoniya a cikin wannan yankin, kuma suna cikin Shirin ko ta kwana.
Haka nan kuma ya bayyana jibge sojoji da Amurkan ta yi a cikin wannan yankin da cewa, yakin kwakwalwa ne da kuma nuna kwanji.
Kakakin sojojin na Iran ya kara da cewa; Mun tabbatarwa da duniya cewa mu ba ‘yan ina da yaki ba ne, amma kuma a lokaci daya ba mu tsoron yaki, domin za mu kare kasarmu cikin karfi da kuma manufofin al’ummar kasar tamu.”
Kakakin sojojin na Iran yana mayar da martani ne akan maganganu marasa tushe da shugaban kasar Amurka ya yi a gaban Majalisar kasar da a cikin ya bayyana Iran da cewa; tana da makamai masu linzamin da za su isa cikin Amurka.