Manyan Hafsoshin soji a kasashen yammacin Afirka, a wani taro da suka gudanar a birnin Freetown na ƙasar Saliyo, a wannan Alhamis, sun jaddada mahimmancin haɗin kai tsakanin ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da ƙawancen ƙasashen Sahel a cikin shirye-shiryen su na kafa rundunar gaggawa ta ECOWAS.
Tattaunawar da shugaban ƙasar Saliyo kuma shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio, ke jagoranta, ta mayar da hankali ne kan tattara sojoji 2,000 nan da ƙarshen shekarar 2026 domin yaƙi da ta’addanci, gami da barazanar da ke fuskantar ƙasashen Sahel.
Mahalarta taron sun jaddada “wajabcin haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin biyu don tabbatar da tsaron yankin,” duk da janyewar ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar daga ECOWAS tare da kafa nasu kawancen.
Ana sa ran ƙasashe membobin za su fayyace gudunmawar da za su bayar na sojoji, tare da mai da hankali kan samun kuɗaɗen kansu da amfani da albarkatun cikin gida kafin neman taimakon waje.
Wannan yunkuri na kafa rundunar gaggawa ta ECOWAS ya zo ne a daidai lokacin da hare-haren ta’addanci ke ƙaruwa a yammacin Afirka.
A cewar ƙididdigar ta’addanci ta duniya, fiye da rabin mace-macen da ke da alaƙa da ta’addanci a duniya a shekarar 2024 sun faru ne a wannan yanki, lamarin da ke nuna bukatar gaggawa na mayar da martani cikin sauri da haɗin kai.