Wata Hukumar Leken Asirin Amurka Ta Yi Watsi Da Zancen Trump Dangane Da Makaman Iran

Hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta musanta zancen Trump na cewa gwamnatin JMI tana kere makamai masu linzami wadanda suke iya kaiwa kasar Amurka.

Hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta musanta zancen Trump na cewa gwamnatin JMI tana kere makamai masu linzami wadanda suke iya kaiwa kasar Amurka.

Jaridar ‘The Nation’ ta nakalto hukumomin leken asiri na Amurka na fadar haka kwanaki biyu bayan da shugaban ya fadi haka a taron hadin guiwa da majalisun dokokin kasar a ranar Laraba.

Kamfanin dillancin Talata  reuters ya bayyana cewa masu sharhi sun bayyana cewa shugaba ya fadi haka ne kawai don bawa kan hujjar farwa kasar Iran da yaki. Har’ila yau wasu kamfanonin watsa labarai na kasar Burtania sun bayyana jawabin Trump dangane da kasar Iran a jawabin san a State of the Union ba zai kasance gaskiya ba, ya kuma wuce gona da iri.

Sun ce wannan maganar ba’a ginata a kan ilmin leken asiri ko wata kafa abin dogaro ba.

A cikin jawabinda Trump yace ‘ Iran tana aiki kan makamai masu linzami wadanda nan gaba kadan suna iya isa Amurka’. Shugaban ya kara da cewa JMI tana sake gina cibiyoyin makamashin nukliya wanda ya riya cewa ya lalatasu a yakin kwanaki 12 a cikin watan Yulin shekara ta 2025..

Zancen shugaban dai ya tunatar da mutane kan yadda Amurka take kaga karya don farwa wata kasa da yaki, kamar yadda shugaba Bus yayi da sunan kasar Iraki tana da makaman kare dangi wanda daga baya bayan ya mamaye kasar Iraki ya tabbata karyace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted