Wata kotu a kasar Faransa ta yanke hukuncin zaman kaso na shekaru 4 kan ba’irania kuma malamar Jami’a Mahdieh Esfandiar bayan ta kamata da abinda ta kira goyon bayan ta’addanci, saboda tana goyon bayan al-ummar falasdinu a Gaza tana kuma allawadai da HKI a yakin da take yi a Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Alhamis ce wata kotu a birnin Paris ta yanke wannan hukuncin, sannan ta haramtawa Esfandiari sake shiga kasar Faransa.
Labarin ya kara da cewa Esfandiari malaman harsuna ne kuma tana da digiri a kan harshen faransanci. Kuma laifinta shi ne rubuta wani abu a shafinta na internet na goyon bayan falasdinawa wanda yin haka laifi ne a kasar Faransa.
A halin yanzu dai esfandiari diyar shekara 39 a duniya zata share shekara guda ne a gidan kaso bayan an share mata shekaru uku da kuma zaman jiran sharia da ta yin a watanni kimani 8.