Wani sabon rahoto ya bayyana yadda Rasha ta dauki matasa daga kasar Kenya sama da 1,000 aikin soja ba bisa ƙa’ida ba tare da tura su Ukraine don yin yaki mai cike da hadari, ba tare cikakken horo ba.
Kafafen yada labarai da dama ciki har da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP sun bankado yadda Rasha ke amfani da dubaru da kuma yaudarar matasa da sunan samar musu da aiki daga Afrika, daga baya kuma a tilasta musu shiga aikin soja da kuma tura su filin daga ba tare da an basu cikakken horo ba.
Wani rahoton binciken hadin gwiwa tsakanin hukumar binciken sirri ta Kenya da kuma hukumar binciken manyan laifuka ta kasar da aka gabatar gaban majalisar dokoki, ya nuna cewa sama da matasan ƙasar 1,000 ne yanzu haka ke filin daga a Ukraine, kuma da dama daga cikin su sun mutu.
Mafi yanwanci ana baiwa matasan Visar yawon bude idao ne a Rasha inda suke bi ta Kasashen Turkiyya ko Hadaddiyar Daular Larabawa, daga baya kuma da aka tsaurara bincike a filin jirgin Nairobi sai Rasha ta koma amfani da wasu asashen Afrika.