rahotanni sun bayyana cewa an zabi iran a matsayin mataimakiyar shugabar kwamitin musamman na majalisar dinkin duniya kan yarjejeniya, kuma mamba ce a ofishin kwamitin.
wannan matakin yazo ne a lokacin taron da aka gudanar a hedkwatar majalisar dake birnin newyork, don haka kasar iran za ta yi aiki a matsayin mataimakiya ga shugabar musamman kan yarjejeiya, kuma zai zama tana da kujera a ofishin,
daga cikin manyan ayyukan da ya doru akan kwamitin shi ne magance matsalolin tsaro da suka hada da kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, sulhunta takaddam cikin lumana da kuma karfafa ci gaba da aiki da dokokin kasa da kasa.
kwamitin zai taka muhummiyar rawa wajen dawo da doka da oda da kuma kokari wajen ganin an kiyaye tsarin dokokin kasa da kasa