Jagora Ya Halarci Wajen Taron Karatun Alur’ani Da Aka yi A Ranar Farko Na Watan Ramadan

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamana’I ya halarci taron karatun Alkur’ani mai tsarki  da aka fara a ranar farko ta Azumin watan

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamana’I ya halarci taron karatun Alkur’ani mai tsarki  da aka fara a ranar farko ta Azumin watan ramadana mai alfarma, tare da manyan mukarraban gwamnati da fitattun makaranta Alkur’ani mai girma da kuma sauran masana ilimin Alkur’ani mai girma.

taron na karatun Alkur’ani mai girma da ake yi a duk watan Ramadan yana nuna irin muhimmiyar rawar da koyarwar alkur’ani ke takawa a rayuwar zamantakewa a jamhuriyar musulunci ta iran , kuma yana kara hadin kai da kankan da kai a lokacin fara Azumin wata mai alfarma.

An gudanar da taron ne a yammacin jiya Alhamis a husainiyar Imam Khumaini dake nan birnin Tehran , kuma kwararrun makaranta Alkur’ani sun yi takarar alkur’ani a gaban jagoran juyin musulunci na iran,

taron yana daya daga cikin muhimman tarukan addini da ake yi a duk wata Ramadan a kasar iran, hakazalika jagoran ya nuna gamsuwarsa game da yadda aka karanta Alkur’ani da sauti mai dadi a lokacin taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted