kungiyar gwagarmayar musulunci ta Hasam tayi Tir da taron da shugaban kasar Amurka ya gudanar na mambobin tabbatar da zaman lafiya a gaza a kasar Amurka, kana ta yi kira da matsawa isra’ila ta dakatar da kai hare-hare a yankin Gaza da kuma bawa falasdinawa yanci cin gashin kansu.
hakazalika kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da su kara kaimi wajen ganin an gaggauta aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana isra’ila kokarin da take yi na kawo cikas.
a jiya ne shugaban Amurka Donald trump ya jagoranci taron da ya kira da sunan mambobin zaman lafiya a birnin Washington DC a cibiyar zaman lafiya ta Amurka,
kasashen dake mambobi a kwamitin sun tare kudi dala biliyan 7don sake gina yankin Gaza, inda trumpa ya sanar da karin tallafin dala biliyan 10 daga bangaren amurka , kuma ya yabawa kasashen da suka halarci wannan taro.