Arif: Hargitsin Bayan-Bayan Nan A Iran Shelanta Yakin ‘Yan Sahayoniya Ne A Mataki Na Biyu Kan Kasar

Mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad Riza Arif ya bayyana cewa, rikice-rikicen bayan nan na Iran, suna a matsayin  shelanta yaki mataki na biyu ne da

Mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad Riza Arif ya bayyana cewa, rikice-rikicen bayan nan na Iran, suna a matsayin  shelanta yaki mataki na biyu ne da ‘yan sahayoniya su ka  yi akan al’ummar Iran,bayan yakin kwanaki 12.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya Ambato mataimakin shugaban kasar ta Iran Muhammad Riza Arif yana cewa wajibi ne a banbanta tsakanin masu koke akan tsadar kayayyaki, wanda hakkinsu ne yin hakan, da kuma masu tayar da hargitsi wanda yake a matsayin yaki ne na “Yan sahayoniya akan al’ummar Iran.

Mataimakin shugaban kasar na Iran ya ce; babban kuskuren da makiya su ka yi shi ne tun a ranakun farko, su ka ingizo da muhimman ‘yan korenku  da hakan ya bai wa jami’an tsaro damar kama su tun da farko. Mataimakin shgaban kasar ta Iran ya kara da cewa kame ‘yan koren da aka yi, ya bayar da damar gano abinda su ka shirye, saboda haka aka dakile ci gaba da barnar da suke yi.

Arif ya kuma ce; Yadda al’ummar Iran ta fito cikin fage, ya taka rawa wajen dakile makircin abokan gabar, kuma ci gaba da kasantuwar al’ummar ta Iran a fage, zai zama mai magance makirce-makircen makiya a kodayaushe.

Sai dai kuma mataimakin shugaban kasar ta Iran ya ce, dakile makarkashiyar da ka yi a yanzu, baya nufin cewa za su daina tunanin kitsa wani makircin da zumma kawo karshen juyin musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted