Dubun Dubatan Alummar Iran Sun Gudanar Da Zanga-zangar Yin Tir Da Masu Tada Tarzoma Da Lalata Dukiyoyi A Fadin Kasar

Rahotanni sun bayyana cewa Alummar kasar iran za su fito kan tituna a yau litinin domin nuna rashin amincewa da kuma yin tir da masu

Rahotanni sun bayyana cewa Alummar kasar iran za su fito kan tituna a yau litinin domin nuna rashin amincewa da kuma yin tir da masu tada tarzoma suna kone-kone da kashe-kashe da kuma lalata dukiyoyin jama’a da ma na gwamnati wadanda suke samu goyon bayan kasashen Amurka da kuma isra’ila , kuma za su nuna goyon bayansu ga jamhuriyar musulunci ta iran.

Mahukumta a iran sun bayyana abubuwan da suka faru a baya bayan nan a matsayin manyan ayyukan taa’ddanci da aka yi kan kasar iran a yan shekarun nan, matakin da kai tsaye Amurka da Isra’ila ke goyon bayan kungiyoyi dake adawa da gwamnatin musulunci ta iran a cikin gida.

 Tarzomar da aka yi ta baya bayannan a iran ta fara ne daga zanga-zangar matsalar tattalin Arziki a birnin Tehran da yan kasuwa suka yi a babbar kasuwar Tehran wadda kan kace kwabo wasu kungiyoyin masu adawa suka karbe ta inda suka yi amfani da makamai wajen hare haren da suka kai a tashin tashinan da aka yi.

Kungiyoyin sun kai hare=haren ta’adanci da ya kai ga mutuwar mutane fararen hula da dama, tare da lalata masallatai bankuna da sauran dukiyoyin alumma, kuma sun yi mummunar barna a garuruwa daban daban na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted