Gwamnatin kasar Jamus ta sanar da kafa wata sabuwar cibiyar ta kare sararin samaniyarta daga kutsen da jiragen sama marasa matuki suke yi.
Hukumar ‘yan sandan kasar ta Jamus ta sanar da cewa a shekarar nan mai karewa fiye da jiragen sama marasa matuki 1,000 ne, su ka yi kutse a sararin samaniyar kasar.
Shugaban bangaren dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan kasar ta Jamus, Holgar Munch ya sanar da cewa; sun iya kididdiga fiye da jiragen sama marasa matuki 1000 da su ka yi shawagi a sararin samaniyar kasar daga farkon wannan shekara zuwa tsakiyar watan nan na Disamba.
Haka nan kuma ya ce, a halin yanzu su da sojojin kasar suna yin bitar yadda za a magance irin wannan kutsen.
Kutsen da aka yi wa Jamus din ya kasance ne a wurare masu muhimmanci ta fuskar tsaro da soja, da su ka kunshi sansanonin soja da kuma filayen jiragen sama, haka nan wasu cibiyoyi kamar tasoshin jiragen ruwa da kamfanoni masu alaka da kere-kere ayyukan tsaro.
Da aka tambaye shi, ko Rasha ce take yin wannan kutsen, jami’in ‘yan sandan ya ce da wuya a iya yanke akan kai tsaye saboda wahalar isa ga wadanda suke sarrafa jiragen, balle a yi musu tambayoyi.
Rasha dai ta sha kore cewa ita ce ke tura jiragen sama marasa matuki zuwa sararin samaniyar kasashen Nato da suke kusa da kuma nesa da ita.