Mataimakin firai minista na kasar Pakistan da Ministan harkokin wajen kasar sun zanta ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a cikin makonni biyu a jare inda suka tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma sauye-sauyen da ake sami a yankin Asia ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa zantawar Senata Muhammad Ishaq Dar da Abbas Aragchi sau biyu a cikin makonni biyu ta wayar tarho ya nuna irin yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake kara karfi.
Labarin ya kara da cewa kasashen biyu suna haka kan iyaka har na tsawon kilomita 909 ga kuma al-adu da tarihi guda da kuma addini da suka hada kasashen biyu. Kasar Iran ce kasa ta farko da ta amince da samuwar kasar Pakistan a lokacinda ta sami yenci daga turawa yan mulkin mallaka a ranar 22 ga watan Augustan shekara 1947.
Harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu a halin yanzu ya kai dalar Amurka biliyon US$2.8, inda kasar Pakistan take sayarwa Iran kayakin da suka kai US$684 miliyon sannan tana shigo da kayaki daga Iran na dalar UA$ 2.1 billiyon. Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin kara bunkasa harkokin kasuwanci, haduwa mutanen kasashen biyu da kuma sadarwa a tsakaninsu. Sannan sun bukaci aiki hadin giwa don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu.