MDD: Burundi Tana Fuskantar matsin Lamba Saboda Yawan ‘Yan Hijira Daga DRC

Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD, ta bayyana cewa; Rikicin da ake yi a kasar DRC ya sa fiye da mutane 84,000 suna

MDD

Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD, ta bayyana cewa; Rikicin da ake yi a kasar DRC ya sa fiye da mutane 84,000 suna gujewa da yin hijira zuwa kasar Burundi.

Hukumar ta ‘yan hijira ta MDD ta kara da cewa; A cikin wannan watan na Disamba ne aka sami kwararar wadannan ‘yan hijirar, wanda shi ne irinsa na biyu a cikin wannan shekarar mai karewa.

Haka nan kuma hukumar ta kara da cewa, kasar ta Burundi ba za ta iya daukar nauyin yawan mutanen da suke kwarara cikinta daga DRC ba.

A baya mutane 70,000 ne su ka yi hijira daga kasar ta DRC zuwa cikin Burundi saboda kaucewa fadan da ake yi, wanda shi ne kwararar mutane mafi yawa a lokaci daya, tun shekaru masu yawa.

Tare da cewa tun a cikin watan Yuni na wanan shekarar ne aka rattaba hannu a tsakanin DRC da Rwanda ta hanyar shiga tsakanin Amurka, sai dai kungiyar M23 da take samun goyon bayan Rwanda tana ci gaba da kai hare-hare.

A bayan nan kungiyar ta M23 ta kame garin  uvira mai mihimmanci, wanda ya jawo suka daga MDD da kasar Amurka.

Kwamitin tsaron na MDD ya yi  kira ga kungiyar ‘yan tawaye ta M23 wacce kasar Rwanda take goyawa baya da ta fice daga cikin garin.

Wannan kiran dai ya zo ne bayan da kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta riya cewa ta janye daga garin Uvira da ta shiga a karshen makon da ya shude.

Sai dai gwamnatin kasar ta DRC ta ce har yanzu M23 ba ta fice daga cikin garin na Uvira ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted