Isra’ila Ta Bada Umarnin Rusa Gidajen Falasdinawa Guda 25 A Yammma Kogin Jodan

Rahotanni sun bayyana cewa isra’ila ta ba wa sojoji umarnin rusa gidajen falasdinawaa guda 25 a sansanin yan gudun hijira dake Nur Shams dake gefen

Rahotanni sun bayyana cewa isra’ila ta ba wa sojoji umarnin rusa gidajen falasdinawaa guda 25 a sansanin yan gudun hijira dake Nur Shams dake gefen tulkaram a arewacin gabar yammacin kogin jodan, a wani shiri da tel aviv ke yi na fadada gine ginen yahudawa  a yankunan falasdinawa ba bisa kaida ba.

Gwamnan garin tulkarm Abdullahi Kamis da yake mayar da martani yayi kira ga majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam da sauran bangarorin diplomasiya da ofisoshin jakadanci da su dauki mataken gaggawa domin dakatar da wannan zalunci.

A ranar juma’a da ta gabata kafafen yada labaran isra’ila sun yi bayanin cewa majalisar tsaron isra’ila ta sanya hannu kan shirinta na kafa haramtattun matsugunnai 19 dake fadin gabar yammacin jodan da isra’ila ta mamaye, a wani mataki da falasdinawa suka ce shirin ne na kara fadada sace filayen su da suka kwashe shekaru suna karewa. Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akalla falasdinawa 232 ne isra’ila ta kashe tare da jikkta sama da 52 a gabar yammacin kogin jodan daga farkon wannan shekarar zuwa yau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted