Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa babu wani mahaluki da zai iya samar da mafita daga wajen yankin da zata ita magance rikicin yankin.
Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a wani taro kan halin da ake ciki a Afghanistan.
“Abubuwan da suka faru a yankin a cikin ‘yan shekarun nan sun nuna cewa shishigi daga kasashen waje su suka kawo illa ga kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa.”
A taron kolin na kasashe makwabtaka da Afghanistan, wanda aka gudanar a Tehran tare da Rasha, Mista Araghchi ya bayyana cewa: “Babu wata mafita ta musamman da za ta iya magance matsalolin yankin da rikicin yankin, kuma mafita daga kasashen waje da kuma shawarwarin da aka yanke daga wasu yankuna ba sa tabbatar da zaman lafiyar kowace kasa.
“Ana iya magance kalubalen yankin ne kawai ta hanyar tattaunawa, shiga tsakani na dukkan kasashe, girmama juna, da kuma hadin gwiwa mai dorewa tsakanin kasashen yankin,” in ji Ministan Harkokin Wajen Iran.
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya ce zaman lafiyar Afghanistan ya dogara ne da haɗakarta cikin tsarin siyasa da tattalin arziki na yanki, yana mai kira da a yi aiki tare tsakanin kasashen makwabta maimakon dogaro da tsoma baki daga waje.
Araghchi ya kuma ce hada kai da Afghanistan cikin harkokin siyasa da tattalin arziki na yankin zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali na dogon lokaci da kuma rage tashin hankali.