A yau Litinin ne Iran ta yaye kallabin sabbin kere-kere na magunguna da aka yi bisa fasahar Nukiliya, a yayin baje kolin kkere-kere karo na 26 a nan birnin Tehran.
A yayin wannan bikin wanda mataimakin shugaban kasar Iran Dr. Muhammad Riza Arif ya halarta, da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa Muhammad Islami, an nuna wasu jerin magunguna da aka yi daga fasahar Nukiliya domin magance ciwon kashi. Wadannan magungunan sun hada; Lu-Alpha-MSH177 da kuma Ga-Alpha-MSH68, sai kuma na’urar da ake amfani da ita wajen yin wadannan magungunan.
A yayin wannan baje kolin an kuma kaddamar da wata cibiya ta kasa domin koyar da fannonin ilimi masu alaka da fasahar Nukiliya.
Daga cikin cutukan da maganin Lu-Alpha-MSH 177 yake yi wa magani da akwai cutar daji mai kisa (cancer). A tsawon lokacin da aka rika yin gwaje-gwaje, maganin ya tabbatar da cewa yana aiki sosai. Kuma shi ne irinsa na farko da aka yi a Iran.
Wannan maganin yana kara tabbatar da yadda Iran din take cin moriyar fasahar Nukiliya ta zaman lafiya.
Sai kuma Ga-Alpha-MSH68 da ake amfani da shi domin daukar hoton yadda cutar daji ( cancer) ta fata take yaduwa, da hakan zai taimaka wajen gano ta da sauri da kuma sanin matakin cutar maras lafiyar.
Ita kuwa na’urar da aka kera, ana amfani da ita ne domin yin magungunan “Themarium 153” da “Lutetium 177” da ake amfani da su domin kashe kwayoyin cutar daji (cancer) ta kashi da rage radadin da mai cutar ke fama da ita.
Samar da wannan na’urar ci gaba ne babba da Iran ta samu a fagen yin magunguna daga sanadarorin Nukiliya.
Wani abu mai muhimmanci da aka kaddamar a wurin wannan bikin, shi ne cibiyar yanar gizo ta ilimin Nukiliya ta kasa,domin bunkasa wannan ilimin a tsakanin ‘yan kasa.