A wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar, ta bayyana cewa an kakkabo jiragen saman marasa matuki da Ukiraniya ta harba zuwa yankin Rostov.
Rahoton na ma’aikatar tsaron Rasha ya kuma ce, wasu yankunan da aka kai wa hare-haren sun kunshi Kamensk-Shaktinsk da kuma Novoshkhtinsk, sai kuma wasu yankuna 9 na gundumar Rostov.
Gwamnan gundumar Rostov, Oblast Yury Slyusar ya bayyana cewa; An sami wasu gine-gine da mutoci da su ka yi illa a yayin hare-haren na drones.
A yankin Kamensky kuwa, harin na Ukiraniya ya yi sanadin lalata wata tashar samar da wutar lantarki.
Haka nan kuma sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta ce, wasu jiragen da Ukiraniya ta harbo guda 38 sun fada a cikin ruwan tekun Caspian.
A wasu yankunan na daban, sojojin Rashan sun sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 16.