Kungiyoyin Falastinawa sun bayyana farmakin Kudus da aikin Jarumtaka

A cikin jawabai daban-daban da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sukayi sun yi marhabin da farmakin da wasu mahara suka kai a jiya Litinin a arewacin birnin

A cikin jawabai daban-daban da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sukayi sun yi marhabin da farmakin da wasu mahara suka kai a jiya Litinin a arewacin birnin Quds, inda suka bayyana hakan a matsayin martani ga kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa take yi kan al’ummar Falastinu, musamman a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Irna, ya nakalto daga shafin tashar talabijin ta Al-Masirah cewa, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai jinjinawa da aikin wanda ta danganta da jarumtaka.

Muna mika gaisuwar bajinta ga farmakin da mayakan gwagwarmayar Falastinawa biyu suka kai a matsugunan yahudawan sahyoniya ta Ramot da ke arewacin birnin Quds da suka mamaye.

Ta kara da cewa wannan farmakin wani martani ne ga laifuffukan ‘yan mamaya da kuma yakin kisan kare dangi da suke yi kan al’ummarmu. »

Hamas ta jaddada cewa wannan mataki na kunshe da sako karara: ga “Shirye-shiryen mamaye Gaza, da kuma masallacin Al-Aqsa.

A nata bangaren, kunmgiyar Jihad Islama ta Falasdinawa ta bayyana wannan aiki a matsayin abin ban mamaki, tana mai imani da cewa yana wakiltar: Martani ga ci gaban manufofin gwamnatin sahyoniyawan masu aikata laifuka, da tsokanar da take ci gaba da yi, da yunkurin da take yi.

A jiya Litinin ce wasu mayakan Falasdinawa biyu suka bude wuta a cikin wata motar safa da ke dauke da mazauna Isra’ila a mahadar matsugunan Ramot da ke arewacin birnin Kudus (Quds), inda suka hallaka 6 daga cikin da raunawa wasu fiye da 10 a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted