Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaran aikinsa na kasar masar badar albadelatty ta wayar tarho inda suka tattauna game da batutuwan da suka shafi yankin da kuma irin ci gaban da aka samu, kuma sun mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi Gaza da kuma shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Iran dai na neman isar da sakon diflomasiyya ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakaninta da kasashen yammacin duniya dangane da shirinta na nukiliya. A halin da ake ciki, Masar ta dauki kanta a matsayin babbar mai shiga tsakani a rikicin Gaza, inda ta daidaita alakar ta da kasashen Larabawa da ke makwabtaka da kasashen duniya.
Kasaashen biyu Iran da Masar suna bin hanyoyin diplomasiyya wajen ganin an dakatar da bude wuta da kuma daukar mataki kan laifukan da HKI ta tafka kan alummar Gaza, game da batun nukiliyar iran kuwa sun yi nuni game da muhimamcin girmama dukkan hakokin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar NPT yadda za su yi amfani da makamashin nukiliya din domin ayyukan zaman lafiya.