Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Lebanon da Iran basa daukan umurni daga Iran. Kamfanin

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Lebanon da Iran basa daukan umurni daga Iran.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Dr Larijani yana fadar haka bayan kammala ziyaran aiki a kasar Iraki. Ya kuma kara da cewa kasashen Iraki da Lebanon suna da asasshen kwarewa a tafiyar da kasashensu. Don haka basa bukatar daukar umurni daga kasarsa.

Sai dai wannan ba zai hana kasashen su shawarci JMI a kan wasu al-amura da suka shafesu ba. A ziyarsa a kasar Iraki dai babban sakataren ya gana da shugaban kasa, firai minister da shugaban majalisar dokoki da kuma tokwaransa na kasar Iraki.

Daga birnin Bagdaza dai ana saran Dr Larijani zai ziyarci kasar Lebanon, inda a cikin yan kwanakin nan kasar ta fada cikin riginginmu na kokarin kwance damarar kungiyar Hizbullah.  

A jawabin da yayiwa yan jaridu kuma Larijani ya ce ba gaskiya bane, gwamnatin JMI tana shishigi a zabubbakan kasar Iraki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments