Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar

Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau Talata, ta wayar tarho a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi.

A cikin wannan makon ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranci yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen Azarbaijan dangane da yankin karabakh a fadar White House. Sannan akwai labarin cewa za’a gina wani babban titi wanda zai ratsa kasashen bitu.

Kasashen dai suna makobtaka da kasar Iran, don haka dangantakarsu na kud da kud da kasar Amurka zai sa Iran ta yi taka tsantsan da su.

A nashi bangaren Aragchi ya taya kasar Armenia murnar rattaba hannu kan yarjeniyar zaman lafiya da Azarbaijan, sannan ya kuma gode mata kan hakkin makobtaka da kasar Iran. Daga karshe ya ce yana fadar Armenia zata kiyaye hakkin kasar a kan Armeniya da kuma kuma yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments