Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa HKI ta so ta lalata kasar Iran ta kuma kifar da gwamnatin JMI, amma ta kasa yin hakan da yardarm All..
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto babban sakataren kungiyar Sheik Naem Qasim yana fadar haka a jiya Jumma’a da yamma. Ya kuma kara da cewa a yakin kwanaki 12 wanda ya fara tun ranar 13 ga watan yuni har zuwa kwanaki 12 ya nuna cewa JMI a shirye take ta fuskanci HKI da Amurka kan mummunan manufofinsu kan JMI.
Da farko sun fake da lalata cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, amma ba shi ne kawai manufarsu ba. Don hukumar IAEA wacce take kula da wadannan cibiyoyin bata bada rahotun cewa Iran tana da shirin gina makaman Nukliya ba. Babbar manufarsu itace ganin bayan tsarin musulunci da ke iko da kasar Iran tun shekaru 46 da suka gabata.
A wani bangare kuma Shiek Qasim ya bayyana cewa, kungiyar ba zata taba mika makamanta ga wani ba musamman a dai dai lokacinda kasar take fuskantar barazana ta, ko ta mika makamanta ko kuma a shafeta da karfi makamai. Ya kammala da cewa Kalmar mika kai bay a cikin kamusimmu. Ko mu yi nasara a kan makiyammu da yardarm All.. ko kuma mu yi shahada a yakarsu bamu da zabi na ukku.