Gwamnatin Mauritaniya Ta Karyata Batun Ganawar Shugaban Kasar Da Fira Ministan Gwmanatin Isra’ila

Rashin amincewar gwamnatin Mauritaniya da al’ummar kasar da duk wani batun neman kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Maganar neman kyautata alaka tsakanin yahudawan sahayoniyya

Rashin amincewar gwamnatin Mauritaniya da al’ummar kasar da duk wani batun neman kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila

Maganar neman kyautata alaka tsakanin yahudawan sahayoniyya da Mauritaniya ya haifar da cece-kuce da kwarara kan titin Mauritaniya, lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta musanta hakan nan take.

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, ganawar da shugaban kasar Mauritaniya Muhammed Ould Sheikh El Ghazouani ya yi da takwaransa na Amurka Donald Trump a fadar White House a karshen makon da ya gabata, a gefen wani karamin taron kolin da ya hada shugabannin Amurka da na yammacin Afirka biyar, ya yi magana kan batun neman daidaita alaka da gwamnatin yahudawan sahayoniyya.

A hukumance, ministan al’adu, fasaha, sadarwa, da kuma hulda da majalisar dokoki, kuma kakakin gwamnati, Hussein Ould Meddou, ya musanta rahotannin da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya Muhammed Ould Sheikh El Ghazouani da ganawa da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a birnin Washington ranar Juma’a.

A cikin wata sanarwa a hukumance, ministan ya tabbatar da cewa rahoton kwata-kwata ba shi da sahihanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mauritania ya ruwaito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted