Kasar Iran Ta Bayyana Cewa: Zabinta Ne Daukan Matakin Da Ya Dace  Idan Aka Sanya Mata Matsin Lamba

Kwamitin Tsaro na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Zabin Iran ne ta daukin duk matakin da ya dace idan aka Sanya mata

Kwamitin Tsaro na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Zabin Iran ne ta daukin duk matakin da ya dace idan aka Sanya mata matsin lamba

Kakakin kwamitin tsaron kasa da manufofin harkokin waje na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da matsin lamba da kasashen Turai ke yi na iya sanya Iran ta dauki matakai kamar ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, da kara inganta makamashin Uranium fiye da kashi 60 cikin 100, da kera manyan na’urorin tace sinadarin Uranium masu inganci, da kuma shiga cikin manyan ayyuykan makamashin nukiliya.

Ibrahim Reza’i, mai magana da yawun Kwamitin Tsaron kasa da manufofin harkokin wajen na Majalisar Shawarar Musulunci, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, yana yin tsokaci game da barazanar Tawagar Turai don kunna hanyar da za ta iya haifar da rugujewa kafin cikar ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231, “Ƙasashen Turai tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya, ba su nuna wani kuduri mai zaman kansa ba kuma sun mayar da martani gaba ɗaya ga matsin lamba irin gwamnatin Amurka musamman a lokacin shugabancin Donald Trump.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments